Hayaniya kan mutum mutumin Jacob Zuma a jihar Imo: Gwamna Rochas yayi raddi ga yan Uba

Hayaniya kan mutum mutumin Jacob Zuma a jihar Imo: Gwamna Rochas yayi raddi ga yan Uba

Gwamnan jihar Rochas Okorocha ya soki jam’iyyar PDP da yi ma asusun gwamnatin jihar Imo karkaf a zamanin mulkin ta, tare da gazawa wajen ciyar da jihar gaba.

Jaridar Premium Times ta ruwaito gwamnan ta bakin kaakakin sa Sam Onwuemeodo yana sukar PDP a ranar Talata, inda yace bata taba gayyatar wani hamshakin mutum zuwa jihar Imo ba.

KU KARANTA: Kishi kumallon mata: Budurwa ta daba ma saurayinta almakashi don yayi hira da wata

“Da a ce a zamanin PDP ne aka yi wannan bako, da sun kulle makarantu da hanyoyi saboda shugaba Jacon Zuma zai zo, haka zalika cikin shekaru 12 da PDP tayi tana mulkin jihar nan bata taba gayyatar wani babbab bako ba, sai dai satar kudin mu tana baiwa yayanta.” Inji Kaakakin.

Hayaniya kan mutum mutumin Jacob Zuma a jihar Imo: Gwamna Rochas yayi raddi ga yan Uba

Gwamna Rochas

Kaakakin yace makasudin zuwan Zuma shine don rattafa hannu kan yarjejeniyar gina kwalejin afirka ta Rochas tsakanin gidauniyar Rochas ta ilimi da kuma gidauniyar Jacob Zuma.

Haka zalika Kaakakin yace ziyarar da Zuma ya kawo ya baiwa manyan yan kasuwa damar tattaunawa da shi akan alakar kasuwanci, cikin su akwai Leo Stan Eketh shugaban Zinox Computers, Pascal Dozie na Bankin Diamond da kuma shugaban kamfanin kera motoci na Innoson da sauransu.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Gwamnan ya sha suka daga jama da dama sakamakon gina mutum mutumin Zuma a jihar a matsayin hanyar karrama shi, musamman yadda karramar tazo kwanaki kadan da kashe wani dan Najeriya a kasar Afirka ta kudu.

Daga karshe Kaakakin yace basu da na sanin gayyato shugaba Zuma, kuma basu bukatar baiwa kowa hakurin yin hakan, inda ya kara da cewa zasu cigaba da gina irin wannan gumaka matukar yin hakan zai kawo ma jihar cigaban da ake bukata.

“Gwamna Rochas ya bude kofofin jihar Imo ga Duniya, kuma yana maraba da duk wani bakon alheri da zai kawo ma jihar cigaba, kuma babu gudu, babu ja da baya,” Inji Kaakakin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel