Madalla: Farashin kayan abinci na cigaba da sauka a Najeriya

Madalla: Farashin kayan abinci na cigaba da sauka a Najeriya

- Hukumar NBS ta kasa tace kayan abinci na rage tsada a Najeriya

- Wata na 8 kenan a jere kayan masarufi na kara araha a Kasar

- Sai dai da zarar an kara albashin ma’aikata za a gamu da matsala

A makon yau mu ka ji daga Hukumar tara alkaluma na kasa watau NBS cewa farashin kayan abinci na cigaba da sauka a Najeriya amma fa akwai danyen aiki a gaba.

A wannan watan dai kayan masarufi sun yi sauki a kasuwa wanda hakan na nuna cewa wata na 8 kenan a jere farashin kaya na sauka kasa a kasar. A halin yanzu dai ana cigaba da girbe kayan abinci a Kasar wanda ke nuna cewa za a samu sauki.

KU KARANTA: Kungiyar Real Madrid za ta bude makaranta a Najeriya

Sai dai kuma karin da ake samu na farashin mai na sa farashin yana zabura. Masana dai sun nuna cewa ba mamaki da zarar an kara albashin ma’aikata a kasar kayan abinci za su kara tashi sama. Amma dai a halin yanzu tattalin kasar na mikewa.

A farkon makon nan aka fara jin kishin-kishin din cewa ana shirin makawa Kasar Iran takunkumin da zai sa man fetur ya kara tsada a kasuwar Duniya. Wannan dai zai sa Najeriya ta samu sauki wajen radadin da ta shiga na tattalin arziki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel