Kishi kumallon mata: Budurwa ta daba ma saurayinta almakashi don yayi hira da wata

Kishi kumallon mata: Budurwa ta daba ma saurayinta almakashi don yayi hira da wata

Wani matashi mai suna Seun ya gamu da ajalinsa a hannun budurwarsa mai suna Adesuna Osazuwa, bayan ta caka masa almakashi a kirji a jihar Legas.

Jaridar Daily Post ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a rukunin gidaje na Gowon, dake Egbeda, jihar Legas, inda masoyan suka samu takaddama bayan ta kama shi yana hira da wata yarinya a manhajar Whatsapp.

KU KARANTA: Gwamnati bata da nufin yi ma Atiku bita-da-ƙulli, gyara muke yi – Inji Hadiza Bala Usman

Sai dai majiyar NAIJ.com ta ruwaito ana zargin yarinyar da kwankwadar kayan maye kafin ta aikinta ma saurayinta wannan ta’asa.

Kishi kumallon mata: Budurwa ta daba ma saurayinta almakashi don yayi hira da wata

Masoyan

Wani ma’abocin facebook yace “Masoyan sun fara fada ne akan zargin cin amana da budurwar ke yi ma saurayin, inda nan da nan ta dauko almakashi ta caka masa a kirji, nan take ya fadi matacce.”

Bincike ya nuna Seuna ya gamu da mutuwarsa a hannun Adesuwa ne, kwanaki biyar bayan ya taya ta murnan zagayowar ranar haihuwarta, inda ya sake jaddada soyayyarsa gar eta a shafin Facebook.

Kishi kumallon mata: Budurwa ta daba ma saurayinta almakashi don yayi hira da wata

Saurayin yayin dayake taya ta murna

A yanzu dai Yansanda sun cika hannu da Adesuwa, yayin daka garzaya da gawar Seun dakin ajiyan gawa. Allah ya shiga tsakanin Nagari da mugu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Yadda shari'ar Nnamdi Kanu ta kasance, kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel