Jita-jitan da ake yadawa game da alluran rigakafi Karya ce – Sultan Abubakar

Jita-jitan da ake yadawa game da alluran rigakafi Karya ce – Sultan Abubakar

- Sarkin musulmi ya karyata masu cewa an gurbata allurar rigakafin shan inna

- Abubakar Sa'ad yayi kira da a sarakunar gargajiya da su taimaka wajen wayar da kan mutane kan mahimmancin yin alluran rigakafi

- Gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al-Makura ya yaba da kokarin sarkin musulmi wajen kawar da wannan cuta daga Najeriya

Mai alfarama Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya yi Allah wadai da jita-jitan da ake ta yadawa akan cewa alluran rigakafin cutar shan inna da wasu cututtuka da ke kashe yara kanana da gwamnati ke badawa gurbatattu ne.

Ya fadi haka ne a taron sanin madafa don kawar da cutar shan inna karo na uku da aka yi a garin Lafia jihar Nasarawa ranar Talata.

Ya ce jita-jitan da ake ta yadawa kan alluran rigakafin wai ya na kashe wasu mutane ko kuma mabiyan wata addini bai haka bane.

Jita-jitan da ake yadawa game da alluran rigakafi Karya ce – Sultan Abubakar

Jita-jitan da ake yadawa game da alluran rigakafi Karya ce – Sultan Abubakar

Saboda hakan yake kira ga masu yada irin wannan mummunar jita-jita da su daina yin haka.

KU KARANTA : Matasan Filato sun rubuta wa Buhari wasika akan hare haren makiyayan Fulani

Sa’ad Abubakar ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya,shugabanin addini da sauran mutanen Najeriya da su taimaka wajen wayar da kan mutane kan mahimmancin yin alluran rigakafi.

Bayan haka gwamna Al-Makura ya mika godiyarsa ga mai martaba sultan Abubakar domin irin goyan bayan da yake badawa wajen kawar da cutar shan inna da sauran cututtuka a kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel