Kuma dai, an sake kai hari a wani ƙauyen jihar Filato, an ƙona gidaje

Kuma dai, an sake kai hari a wani ƙauyen jihar Filato, an ƙona gidaje

Rundunar Yansandan jihar Filato ta tabbatar da sake kai wani sabon hari a kauyen Rotsu a ranar Litinin 16 ga watan Oktoba, dake gab da garin Nkyie a cikin karamar hukumar Bassa, inji rahoton Premium Times.

Abin mamakin shine an kai wannan hare hare ne duk dokar hana fita da aka kaddamar a karamar hukumar Bassa, daga safe har dare tun a ranar Juma’a.

KU KARANTA: Rahama Sadau ta yi zarra: Tashin farko, Rariya ya kere ma Mansoor, Dan Kuka da Zinaru a masana’antar Kannywood

Kaakakin rundunar Yansandan jihar Terna Tyopev yace an kai hari a kauyen Rotsu a ranar Litinin, amma ba’a kashe kowa ba, illa dai an kona gidaje 3, “Amma Yansanda sun kai agaji” Inji shi.

Kuma dai, an sake kai hari a wani ƙauyen jihar Filato, an ƙona gidaje

Yansanda

Hakazalika Kaakakin yace Yansanda sun kawar da wani hari da aka yi kokarin kaiwa a wani kauye dake karamar hukumar Riyom duk a daren Litinin, bayan sun samu kira daga jama’a garin.

A ranar Talata 17 ga watan Oktoba ne gwamnan jihar, Simon Lalong ya kai ziyar garin da aka kai harin, tare da rakiyar kwamishinan Yansanda Adie undie, inji majiyar NAIJ.com.

Daga karshe Kaakakin yace kwamishinan ya umarci duk wani dansanda a jihar da yayi shirin ko ta kwana, don tunkarar duk wani barazanar hari a jihar Filato.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel