Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin Buhari ta kawar da Talauci

Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin Buhari ta kawar da Talauci

- Majalisar dattawan Najeriya tayi kira da kawar da Talauci a Najeriya

- Yan Majalisar sun bukaci shugaba Buhari ya zage damtse wajen gudanar da ayyukan jin kai

Majalisar dinkin Duniya ta shawarci gwamnatin tarayya data yi hubbasa wajen ganin ta kawar da talauci daga kasa Najeriya, inda ta koka da alkalumman da wata hukumar gwamnati ta fitar, inda tace talakawan Najeriya sun kai miliyan 120.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan matsaya ta Majalisar dattawar ya biyo bayan wani kuduri da Sanata Ali Wakili ya gabatar gaban majalisar tare da wasu Sanatoci 22 a ranar kawar da talauci ta Duniya, wanda majalisar dinkin Duniya ta tsayar.

KU KARANTA: Ýan ƙasa Nagari dake amfana da shirin N-Power sun bada agajin kujeru da tebura ga makarantar Firamari (Hotuna)

Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta dage a kokarin da take yi musamman ta bangaren tsare tsaren data kirkiro na tallafa ma yan Najeriya, musamman, mata, matasa da gajiyayyu.

Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin Buhari ta kawar da Talauci

Majalisar Dattawa

Dayake goyon bayan kudirin, Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano ya bayyana talauci a matsayin wani makamin kare dangi, wanda maganinsa kawai shine gyara tattalin arzikin kasa, inji majiyar NAIJ.com.

A nasa jawabin, Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu yace akwai bukatar gwamnati fa fada tsarin habbaka kamfanunuwa dake kasar nan, tare da tatsar masu arziki ta hanyar daura musu haraji don taimakon talakawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Shugaban IPOB ya tsere, kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel