Dalilin da yasa zan cire hannu na akan shari'ar Nnamdi Kanu - Mai Shari'a Nyako

Dalilin da yasa zan cire hannu na akan shari'ar Nnamdi Kanu - Mai Shari'a Nyako

Mai shari'a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja, ta yi barazanar cire hannun ta daga shari'ar Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara ta IPOB.

A yayin jawabi wajen gudanar da shari'ar ta a ranar Talatar yau, Alkaliyar ta bayyana cewa akwai barazanar da take fuskanta wajen masu wakiltar Kanu dake kokarin fusatar da ita.

Mai Shari'a Nyako ta yi wannan gargadin ne sakamakon cacar baki da ta balle tsakanin ta da lauyoyin shugaban na IPOB a yayin gudanar da shari'a.

Dalilin da yasa zan cire hannu na akan shari'ar Nnamdi Kanu - Mai Shari'a Nyako

Dalilin da yasa zan cire hannu na akan shari'ar Nnamdi Kanu - Mai Shari'a Nyako

Wannan cacar baki ta barke ne yayin da lauyan Kanu Ifeanyi Ejiofor ya shigo da wani batu a gaban lotun wanda bisa tsari ya kamata ya shigar da shi tun a fari.

KARANTA KUMA: Wadanda Shugaba Buhari ya nada mukamai sun sabawa 'Yan Majalisa

Mai shari'ar yayin mayar da martani ga lauyan na Kanu ta ce, wannan izgili da lauyan ya ke yiwa kotu ya kai ta makura saboda in har ba sa bukatar ta cikin wannan al'amari sai ta cire hannun ta daga shari'a tun kafin ta yi nisa.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel