'Yan damfara suna amfani da sunan Magu suna kwatar kudi — EFCC

'Yan damfara suna amfani da sunan Magu suna kwatar kudi — EFCC

- 'Yan damfara suna anfani da sunan shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu suna kwatar kudi

- Hukumar tayi gargadi ga mutane tun da dadewa

- Hukumar tayi kira ga shugabanni su lura da irin wasikar da ake aiko musu da sunan Magu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara jawa jama’a kunne game da ‘yan danfara masu anfani da sunan shugaban hukumar Ibrahim Magu suna kwatar kudi.

Daga bakin mai magana da yawun hukumar ne, Mista Wilson Uwujaren ya shaida cewa an dade ana nanatawa mutane su dinga lura da irin wadannan ‘yan damfaran. Irin mutanen da suke danfara sune ministoci, gwamnoni da wasu manyan ciyamomi na jam’iyyu

'Yan damfara suna amafani da sunan Magu suna kwatar kudi — EFCC

'Yan damfara suna amafani da sunan Magu suna kwatar kudi — EFCC

‘Yan danfarar suna fakewa da rubuta wasika suna aikawa manyan shugabannin da suke aikin almundahana da hukumar take tuhuma. Suna aika musu da wasikar gayyata zuwa ofishin nasu da sunan Ibrahim Magu.

Duk da gargadin da hukumar tayi bai hana ‘yan danfarar cigaba da sana’ar su ba. A cewar Uwujaren ne ‘akwai sanda a baya ‘yan danfarar ke yaudarar mutane ta yanar gizo a shafukan Facebook da sunan Magu suna karbar cin hanci daga wasu manyan shugabanni.'

DUBA WANNAN: Kungiyar kwadago ta ki karbar tayin naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi

Hukumar yaki da cin hanci tana so ta shaidawa mutane ba hannunta a cikin wannan irin muguwar damfarar, kuma Magu bai rubuta ko ya sa wani ya rubutawa wani gwamna ko shugaba wasika ba.

Mista Uwujaren ya yi kira ga mutanen da ake yiwa barazanar karbar cin hanci da su sa ido kuma su tabbatar da duk wata wasika da ta fito ta gayyata da sunan shugaba Magu da sa hannun shi ce ba ta ‘ayan danfara ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel