Wadanda Shugaba Buhari ya nada mukamai sun sabawa 'Yan Majalisa

Wadanda Shugaba Buhari ya nada mukamai sun sabawa 'Yan Majalisa

- Rikici na nema ya kaure tsakanin 'Yan Majalisa da Fadar Shugaban kasa

- Wasu da aka ba mukami sun fara aiki ba tare da zuwa gaban Majalisa ba

- Hakan dai ya sabawa tsarin mulkin Najeriya kuma Majalisar ta yi gargadi

Ba mamaki wani sabon rikici ya kaure tsakanin Majalisar Dattawa da Fadar Shugaban kasa kamar yadda mu ke samun labari daga Daily Trust.

Wadanda Shugaba Buhari ya nada mukamai sun sabawa 'Yan Majalisa

Shugaban Hukumar FERMA ya saba dokar Majalisa

Wasu da Shugaban Kasar ya ba mukami sun shiga Ofis ne ba tare da zuwa Majalisa ta tantance su ba. Daga cikin wadanda su ka saba dokar akwai Shugaban Hukumar FERMA Nuruddeen Rafindadi da kuma NLRC na kasa Lanre Gbajabiamila.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari zai bar Najeriya

'Yan Majalisar dai sun ce bai hallata wadanda aka ba mukamin su fara aiki ba tare da bi ta Majalisa ba. Dokar Hukumomin dai sun nuna cewa dole sai Majalisar Dattawa ta tantance duk wanda Shugaban kasar ya zaba.

Mai magana da bakin Sanatocin Kasar Aliyu Sabi Abdullahi yayi gargadi kwanaki game da irin wannan sabawa doka. A baya dai an ta samun takaddama tsakanin Fadar Shugaban kasar da kuma Sanatocin Najeriya saboda nadin Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel