Ku taimaka ku tsame sunana daga cikin wadanda suka tsayawa Kanu; Sanata Abaribe ya roki kotu

Ku taimaka ku tsame sunana daga cikin wadanda suka tsayawa Kanu; Sanata Abaribe ya roki kotu

Sanata mai wakiktar mazabar Jihar Abiya ta kudu, Eyinaya Abaribe, ya aikewa kotu takardar neman ta tsame shi daga cikin wadanda suka tsayawa gudajjen shugaban kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu.

A takardar da aka aikewa gwamnatin tarayya ta hannun kotu, Nnamdi Kanu, da wanda ya tsaya masa, Sanata Abaribe, suna neman kotu data tsame sunan Sanata Abaribe daga cikin masu tsayawa Kanu tare da cire shi daga cikin sharudan bayar da belin Kanu.

Ku taimaka ku tsame sunana daga cikin wadanda suka tsayawa Kanu; Sanata Abaribe ya roki kotu

Ku taimaka ku tsame sunana daga cikin wadanda suka tsayawa Kanu; Sanata Abaribe ya roki kotu

Abaribe na neman kotu data dawo masa da miliyan 100 da duk wata kadara da ya bayar kafin ta bayar da belin Kanu tunda har yanzu ba a san inda Kanu yake ba tun bayan da sojoji suka birkice gidan na Kanu.

Abaribe ya bayyana cewar yanzu bashi da alhakin nemowa kotu Kanu tunda gwamnati ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ta'addanci. Saboda haka yanzu alhakin gabatar da Kanu gaban kotu yana wuyan jami'an tsaron Najeriya.

DUBA WANNAN: An zabi Najeriya domin wakiltar Afrika a hukumar kare hakkin bil-adam ta duniya

Wannan korafi na Abaribe yanzu haka yana gaban mai shari'a Binta Nyako dake babbar kotu a Abuja domin sauraro.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar zata tisa keyar wadanda suka tsayawa Kanu zuwa gidan yari matukar suka gaza gabatar dashi gaban kotu kamar yadda suka amince kafin karbar belinsa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel