Hadarin dake tattare da masu neman lafiya a wasu asibitocin kasar Masar

Hadarin dake tattare da masu neman lafiya a wasu asibitocin kasar Masar

A wani rahoto na ranar Laraba 11 ga watan Oktoba da gwamnatin kasar Najeriya ta fitar, ta na gargadin al'ummar Najeriya dake fita kasashen ketare domin neman lafiya kasancewar wasu aibitocin kasar Masar dake satar sassan jikin dan Adam domin cin ma wata manufa ta su.

Wannan rahoton ya zo ne daga ministrin lafiya da sanadin likitan gwamnatin tarayya Dakta Wapada I. Balami, sakamakon wasu asibitocin kasar masar dake sace sassa musamman koda domin yin dashen ta jikin wasu mabuktan dake siyansu da makudan kudi.

Wasikar gargadi daga gwamnatin Najeriya kan wasu asibitocin kasar Masar dake satar sassan jikin dan Adam

Wasikar gargadi daga gwamnatin Najeriya kan wasu asibitocin kasar Masar dake satar sassan jikin dan Adam

Hukumar tsaro ta kasar Misra ta yi nasarar cafke mutane 41 dake da hannu cikin aikata wannan laifi, yayin da gwamnatin Najeriya ta samu rahoto kuma take gargadin 'yan Najeriya akan lura da wadannan asibitoci guda hudu kamar haka; Dar al-shefa na garin Helwa, Asibitin Albashar Specialist dake garin Faisal Giza, Cibiyar lafiya da aikin tiyata ta Al-Amal dake Giza da kuma asibitin Dar Ibn Al-Nafis dake garin Giza dukkaninsu a kasar Masar.

KARANTA KUMA: Kungiyoyi 10 masu karfin gaske a Najeriya

A wasikar da gwamnatin tarayya ta wallafo domin gargadin 'yan najeriya akan daukar izina da wannan asibitoci, ta na kuma jan kunnen likitocin Najeriya akan su dage da baiwa marasa lafiyansu masu fita kasar Misra shawara domin lura don gujewa fadawa hannun miyagu.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel