Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

Yanzu Yanzu: Bazan taba komawa PDP ba - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba zai taba komawa jam’iyyar PDP ba

- Ya bayyana hakan ne bayan ganawar sirri da yayi tare da shugaban jam’iyyar

A ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yace Najeriya na bukatar jam’iyya mai shugabanci mai karfi da kuma jam’iyyar adawa mai karfi domin samun gwamnatin damokradiya a kasar.

Mista Obaanjo ya bayyana hakan yayinda yake magana da yan jarida jim kadan bayan ya karbi bakuncin shugban jam’iyyar PDP na kasa, Ahmed Makarfi a garin Abeokuta.

KU KARANTA KUMA: Yadda ake amfani da kungiyoyi wajen satar kudaden - Ngozi Okonjo-Iweala

Tsohon shugaban kasar wadda ya bayyana cewa ya janye daga siyasar jam’iya, yace wannan hukunci ba zai shafi soyayyar da yake na son ganin cigaban Najeriya ba.

Tsohon shugaban kasar yace: “Bazan taba komawa jam’iyyar PDP ba, kamar yadda kare ba zai taba komawa ga aman sa ba.”

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel