Shugaba Buhari zai tafi wani taro Kasar Turkiyya

Shugaba Buhari zai tafi wani taro Kasar Turkiyya

- Shugaban Kasa Buhari zai yi wata tafiya zuwa Kasar waje

- Za ayi wani taro a Kasar Turkiyya inda Shugaban zai halarta

- A yau ne dai Shugaban kasar zai bar Najeriya zuwa Kasar

Labari ya iso mana daga Fadar Shugaban kasa cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wata tafiya zuwa Kasar waje.

Shugaba Buhari zai tafi wani taro Kasar Turkiyya

Baba Buhari zai kara wata tafiya kasar waje

Kamar yadda Garba Shehu ya bayyana Shugaban zai bar Najeriya ne a yau domin wani taro da za ayi a babban Birnin Kasar Turkiyya na Ankara. A taron Shugaba Buhari zai gana da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Erdogan game da sha’anin da su ka shafi kasashen biyu.

KU KARANTA: Najeriya ta samu matsayi a gaban Duniya

Za dai ayi taron ne da sauran kasashen Duniya masu tasowa 8 a Ranar Juma’a inda zai gana da Shugabannin Kasar Masar, Malaysia, Fakistan, Iran da irin su Bangladesh da sauran su. Shugaba Buhari zai kuma gana da Shugaban Majalisar Ismail Kahraman.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel