Sabon rahoto ya nuna shugaba Buhari na aiki kan tattalin arziki, sai dai talaka dai baya ji a jika

Sabon rahoto ya nuna shugaba Buhari na aiki kan tattalin arziki, sai dai talaka dai baya ji a jika

- Sabon rahoto ya nuna tun watan 2 na bana, farashin kayayyaki suka dena hauhawa, sai dai sauka

- Gwamnatin APC ta dage kan lallai tana aiki, jam'iyyun adawa kuma sun ki yarda ana ci gaba

- Jama'a dai har yanzu basu daina kokawa ba, ganin har yanzu akwai talauci a kasa

A yau talata, hukumar kididdiga ta kasa, ta fitar da sanarwa, cewa tun daga watan biyu, farashin kayayyaki basu kara hawa ba a Najeriya, sai ma dai sauka da suke yi, inda a watan jiya, suka sauka da kusan kashi 15 bisa 100.

Sabon rahoto ya nuna shugaba Buhari na aiki kan tattalin arziki, sai dai talaka dai baya ji a jika

Sabon rahoto ya nuna shugaba Buhari na aiki kan tattalin arziki, sai dai talaka dai baya ji a jika

A baya ma dai, kididdigar ta nuna tattalin arzikin na kasa na kara farfadowa, da kusan kashi 2 bisa dari, a maimakon tsukewa da yake tayi a baya, tun farkon shekarar 2015. Wannan na nuin gaba zata fi baya kyau a irin tsarin da ake kai.

Kididdigar dai ana dauka wata-wata ne, domin a tantance ci gaban da aka sami ko akasin haka. Ana kuma sake sakin rahoton a watanni hudu, wanda ake kira kwata. Sai kuma a hada na rabin shekara, da na shekara a gwada da na baya.

DUBA WANNAN: Najeriya ta sami shiga kwamitin kare hakkin binAdama na duniya

Matsalar dai da gwamnatin APC ke fuskanta, shine, bakunan da yawa, su kuma talakawa a kasa suke so su gani, ba a takardun turanci ba. Har yanzu dai ana ganin karuwa masu barace-barace a kan tituna, daga yara da mata, har matan aure.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel