'Yan Bindiga sun yi garkuwa da DPO da wasu mutane 5 a Jihar Neja

'Yan Bindiga sun yi garkuwa da DPO da wasu mutane 5 a Jihar Neja

- Sun kama DPO da Odilin sa da wasu mutum 4 a kan hanyar su ta zuwa Minna

- Sun bukaci kudin fansa na naira miliyan 16

- Harshashen da suka harba ya kashe wani mai tireda tare da jikkata wata mai ciki

Da safiyar ranar Lahadi ne 'yan bindiga suka kama DPO na ofishin 'yan sandan Sarkin Pawa da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja, tare da Odilin sa da wasu mutane 4 a kan hanyar su ta zuwa Minna.

'Yan Bindiga sun yi garkuwa da DPO da wasu mutane 5 a Jihar Neja

'Yan Bindiga sun yi garkuwa da DPO da wasu mutane 5 a Jihar Neja

An ruwaita cewa 'yan bindigan sun harba bindiga don su razana masu wucewa amma sai wasu harsasai suka balle suka kashe wani mai tireda nan take tare da jikkata wata mai ciki wanda a halin yanzun take jinya a asibiti.

DUBA WANNAN: Allah Sarki! Wani mai fama da cutar Kyandar Biri ya kashe kan sa

An samu rahoton cewa 'yan bindigan sun bukaci kudin fansa na naira miliyan 16 kafin su saki garkuwan na su.

A lokacin tattara wannan rahoto, Adewale Babalola wanda shi ne mai magana da yawun Hukumar 'yan sandan jihar Neja, ya ce ba zai samu daman yin magana ba saboda ya na cikin zauren tattaunawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel