Fani-Kayode yayi tsokaci akan maganar da Buhari yayi game da kisan Filato

Fani-Kayode yayi tsokaci akan maganar da Buhari yayi game da kisan Filato

- Fani Kayode ya soki jawabin Buhari akan kisan filato

- Tsohon ministar ya ce shugaban kasa yaki jajantawa iyalan mutanen da aka kashe a Filato

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaba jami'an tsaro umarnin hana mayar da martani a Filato

Tsohon ministar sufurin jirgin sama, Femi Fani-Kayode ya soki shugaban kasa Muhammadu Buhari akan maganar da yayi game da kisan da aka yi a Filato.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kisan da aka yi a wata kauye a jihar Filato,da cewa al’amarin ya wuce gona da iri.

Fani-Kayode yayi tsokaci akan maganar da Buhari yayi game da kisan Filato

Fani-Kayode yayi tsokaci akan maganar da Buhari yayi game da kisan Filato

Shugaban kasa ya ba jami’an tsaro umarni da su tabbatar da tsaro a jihar, da kuma hana mutane daukan fansa.

KU KARANTA : Zaben 2019 : Oyegun ya mayar wa Bisi Akande martani akan maganar da yayi na rashin ba Buhari atomatik tikitin takara

Amma Fani-Kayode ya soki Buhari da cewa, yayi mamaki irin kalaman da Buhari yayi.

Fani-Kayode ya rubuta a shafin sa na tuwita cewa, “ A jiya ne Musulmai makiyayan Fulani suka kashe kristoci 40 wanda ya kunshi mata da kananan yara a jihar Filato

“Shugaban kasa @Buhari yaki jajantawa iyalan wadanda aka kashe.

“Amma ya fito yace kada a mayar da martani akan yan uwan sa Fulani, saboda Allah wani irin shugaba ne wannan?, inji Fani-Kayode.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel