Fayose da wasu kusoshin Kudu Maso yamma sun gana domin tantance shugaban jam'iyyar PDP

Fayose da wasu kusoshin Kudu Maso yamma sun gana domin tantance shugaban jam'iyyar PDP

Wasu kusoshin jam'iyyar PDP reshen Kudu Maso Yamma sun fara tattaunawa domin samun yarjejeniya wajen tantance shugaban jam'iyyar PDP na kasa sakamakon taron jam'iyyar na watan Dasumba mai gabatowa.

Wannan taro da gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya jagoranta, an gudanar da shi ne a Otel din Renaissance dake jihar Legas daren ranar Litinin din da ta gabata, inda mahalarat taron suka amince da ci gaba da halarta taruka daban-daban anan gaba domin cin ma manufarsu a taron jam'iyyar ta kasa mao gabotowa.

NAIJ.com ta fahimci cewa, baya ga gwamnan jihar Ekiti, sauran mahalarta taron sun hadar da tsohon gwamnan jihar Oyo rashidi Ladoja, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa Cif Borde George, tsohon minista Labarai Dapo Sarumi da kuma tsohon shugaban jam'iyyar ta PDP reshen Kudu Maso Yamma Tajudeen Oladipupo.

Fayose da wasu kusoshin Kudu Maso yamma sun gana domin tantance shugaban jam'iyyar PDP

Fayose da wasu kusoshin Kudu Maso yamma sun gana domin tantance shugaban jam'iyyar PDP

Fayose ya bayyana cewa, "ya kira wannan taron ne domin kowa ya kawo ta shi gudunmawar don a samar da yarjejeniya guda a tsakaninsu. Ya ke cewa bai dace shugabannin jam'iyyar PDP reshen Kudu maso yamma su shiga taron jam'iyyar na kasa ba ba tare da hadin kawunansu wri guda ba."

KARANTA KUMA: Kungiyoyi 10 dake girgiza gwamnatin Najeriya

Gwamnan jihar Ekiti ya kara da cewa, tarukan gaba da za su gudanar zai hadar da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar reshen Kudu maso Yamma domin su tsayar da mutum guda da za su marawa baya a taron kasa.

A fahimtar NAIJ.com, yanzu lokaci ne na jam'iyyar PDP ta fitar da shugabanta daga yankin Kudu Maso Yamma, wanda a yanzu masu nuna sha'awarsu ta shugabantar jami'yyar daga wannan yanki sunhadar da tsohon mataimakin jam'iyyar na kasa Borde George, tsohon gwamnan jihar Ogun Otunba Gbenga Daniel da kuma tsohon ministan ilimi Farfesa Tunde Adeniran.

An samu rashin sa'a Daniel da Adeniran ba su halarci wannan taro ba, sai dai Fayose ya na tabbaci halartarsu a taro na gaba.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel