Kungiyar Kwadigo ta nemi a rushe gunkin Jacob Zuma da Rochas ya gina

Kungiyar Kwadigo ta nemi a rushe gunkin Jacob Zuma da Rochas ya gina

- Kungiyar ta ce zuma bai cancanci wannan karamci ba

- Ta kuma ce tsayar da gunkin shirmen banza ne da cin mutumcin jama'ar Jihar Imo

- Ta bukaci Gwamnan ya yi gaggawan sauke gunkin kuma ya nemi afuwan mutane

Kuniyar Kwadago ta Najeriya wato ULC, ta yi Allah wadai da Gunkin Shugaban Kasar Afirika ta Kudu, Jacob Zuma, da Rochas Okorocha ya mikar tare da bai wa wani titi sunan Shugaban Kasan a garin Owerri ta Jihar Imo.

Kungiyar Kwadigo ta nemi a rushe gunkin Jacob Zuma da Rochas ya gina

Kungiyar Kwadigo ta nemi a rushe gunkin Jacob Zuma da Rochas ya gina

Kungiyar ta bukaci a sauke gunkin saboda darajanta Zuma shirmen banza ne kuma cin fuska ne ga mutanen Jihar Imo baya ga cece-kucen da hakan zai janyo tsakanin 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Abun da za mu yi wa kasashen da su ke jinkirta bai wa 'yan Najeriya Visa - Gwamnatin Tarayya

Shugaban Kungiyar mai suna Mr Joe Ajaero ya yi kira ga al'ummar Jihar Imo da sauran masu kishin Kasa da su bukaci Gwamnan ya yi gaggawan sauke gunkin tare da neman afuwar mutane kuma ya dawo wa Jiha kudin da ya kashe wurin aikata wannan abun kunya.

Kungiyar ta ce ko kusa Zuma bai cancanci wannan karamci ba don babu wata gudummuwa da ya bayar wurin cigaban Najeriya ko Jihar ta Imo.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel