Abun da za mu yi wa kasashen da su ke jinkirta bai wa 'yan Najeriya Visa - Gwamnatin Tarayya

Abun da za mu yi wa kasashen da su ke jinkirta bai wa 'yan Najeriya Visa - Gwamnatin Tarayya

- Gwamnatin Tarayya ta bayyana matakin da zata dauka kan kasashen da su ke hana 'yan Najeriya Visa

- Ta bayyana hakan ne a wani taro da manyan jam'ian Gwamnatin su ka yi

- Ta ce zata yi ramuwa ga duk kasar da ta jinkirta bai wa 'yan Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta dau alwashin ramuwa ga duk kasar da ta jinkirta bai wa 'yan Najeriya visa ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Hakan sakamakon wani taro ne da jiga-jagan jam'ian Gwamnati su ka yi.

Taron ya samu halartar Ministan Harkokin Kasashen Waje, Laftana Janar Abdulrahman Dambazau (Murabus), da Alkalin Alkalai na Kasa wato Geoffrey Onyeama, da Ministan Shari'a wato Abubakar Malami sai kuma Kwanturola Janar na imigireshon Mohammed Babandede.

Abun da za mu yi wa kasashen da su ke jinkirta bai wa 'yan Najeriya Visa - Gwamnatin Tarayya

Abun da za mu yi wa kasashen da su ke jinkirta bai wa 'yan Najeriya Visa - Gwamnatin Tarayya

Dambazau ya ce dole a magance jinkirin da wasu kasashe ke yi na bai wa 'yan Najeriya visa don abun ya fara zama raini. Ya kuma ce cikin murya kakkausa, kasashen su daina tunanin bukatar su da mu ke yi ta fi wacce su ke mana ne.

KARANTA KUMA: Taurin bashi: Za a dawo da zakakuran daliban Najeriya 100 daga Birtaniya

Shi kuwa Babandede cewa ya yi dole mu kare mutuncin kasar mu ta hanyar mayar da martini ga wata kasa da ta jinkirta bai wa 'yan Najeriya Visa. Ya kara da cewa Najeriya ta jajirce wurin tabbatar da amintaccen alaka tsakanin ta da kasashe.

Onyeama kuwa ya bayyana cewan an yi zaman ne don samar da mafita ga matsalolin da 'yan Najeriya ke fuskanta wurin samun Visa na kasashe. Ya ce saboda lamarin jakadanci ne, su da duk hukumomin da abun ya shafa za su hadu su samar da mafita.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel