Gwamnatin Tarayya ta bayyana abin da ya sa za ta ci bashi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana abin da ya sa za ta ci bashi

- Gwamnatin Buhari na kokarin karbo wasu bashi a Duniya

- Ministar Kudi na kasar ta bayyana abin da ya sa za ta ci bashi

- Adeosun tace hakan ya zama dole kuma ba facaka za ayi ba

Bashin da ke wuyan Najeriya ya karu daga 2015 zuwa yanzu don kuwa a yanzu ana bin Najeriya bashin sama da Dala Biliyan 15.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana abin da ya sa za ta ci bashi

Gwamnatin Buhari za ta kara cin bashi

Sai dai kuma kwanan nan aka ji cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa Majalisa takarda inda yake neman iznin karbo bashin Dala Miliyan 5.5. Ministar kudi Kemi Adeosun ta bayyana abin da ya sa Gwamnatin Kasar ke shirin cin wasu bashin.

KU KARANTA: An taso wasu Gwamnonin Kudu a gaba

Kemi Adeosun ta bayyana wannan ne bayan wani taro da ta halarta a Hukumar IMF mai bada lamuni ta Duniya. Ministar tace Gwamnatin Buhari tana bi a hankali wajen karbo bashi a kasar kuma ba za ayi facaka da kudin ba.

Ministar tace za ayi amfani da kudin ne wajen gina titi da kuma hanyar jirgin kasa. Ministar tace matsin da aka shiga na tattali ya hana a kara haraji a kasar. Nan gaba dai idan abubuwa su ka mike Najeriya za ta rage cin bashi Inji Ministar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel