Jama'a sun soki Gwamnan Jihar Ribas da na Jihar Imo

Jama'a sun soki Gwamnan Jihar Ribas da na Jihar Imo

- Jama'a sun yi ca a kan Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha

- Gwamnan ya gayyata Jacob Zuma na kasar Afrika ta Kudu

- Haka kuma Gwamnan Ribas ya harba kasar Sifen kallon kwallo

Mun fahimci cewa Jama'a na ta sukar Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike da na Jihar Imo Rochas Okorocha kwanan nan.

Jama'a sun soki Gwamnan Jihar Ribas da na Jihar Imo

Gwamnan Jihar Ribas tare da 'Yan wasan Real Madrid

Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha ya gayyato Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma Jihar sa inda aka nada masa sarauta sannan kuma aka kaddamar da wani titi da sunan sa tare da gina wani mutum-mutumin sa.

KU KARANTA: Wasu 'Yan kasar waje sun yi hadari a Birnin Abuja

Jama'a sun soki Gwamnan Jihar Ribas da na Jihar Imo

An karrama Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jihar Imo

Sai dai Gwamnan ya kashe makudan kudi wajen yin wannan abu da aka rasa gane tasirin sa. Inda shi kuma Gwamnan Jihar Nyesom Wike ya taka ne har Kasar Sifen inda su ka kalli wasan Kungiyar Real Madrid tare da wasu abokan sa.

Ba wannan ne karo na farko ba dai Wike ya tafi kallon wasan Real Madrid amma wannan karo an hange sa tare sa n bayan 'Yan wasa irin su Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos amma ya bayyana cewa yana kokarin ganin Kungiyar ta kafa Makarantar kwallon kafa ne a Jihar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel