Bashin Dala biliyan 5.5: Jam'iyyar APC ta mayar wa da PDP martani

Bashin Dala biliyan 5.5: Jam'iyyar APC ta mayar wa da PDP martani

Jam'iyyar APC mai mulki ta yi fata-fata da jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bisa zargin ta da tayi da yin kokarin ciyo wa kasa bashin makudan kudaden da suka kai Dala Biliyan 5.5 da nufin gudanar da ayyukan ci gaba.

Jam'iyyar ta yi wannan martanin ne a cikin wata sanarwar manema labarai dai mai magana da yawun jam'iyyar na kasa Bolaji Abdullahi ya fitar a jiya Lahadi inda ya bukaci jam'iyyar ta PDP da ta farka ta bude idon ta ga sabbin dabaru da hanyoyin samun kudade na zamani.

Bashin Dala biliyan 5.5: Jam'iyyar APC ta mayar wa da PDP martani

Bashin Dala biliyan 5.5: Jam'iyyar APC ta mayar wa da PDP martani

KU KARANTA: Kungiyar Real Madrid ta kafa muhimmin tarihi

NAIJ.com ta samu dai cewa tun farko jam'iyyar ta PDP ta yi kaca-kaca da jam'iyyar APC din ne bisa abun da suka kira yawan bashin da jam'iyyar ke ciyo wa kasar babu gaira-babu dalili.

To sai dai da take kare kanta, jam'iyyar mai mulki ta APC ta bayyana cewa bashin da gwamnatin ta Buhari ke nema daga kasashen waje ya zama dole ne sakamakon wawure baitul malin kasar da akayi lokacin mulkin jam'iyyar a shekarun baya.

Mai kara tu dai zai iya tuna cewa a satin da ya shude ne dai shugaba Buhari ya aikewa majalisar dattijai da wata takarda dauke da bukatar sa ta ciyo bashi daga kasashen waje.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel