Shiriya daga Allah: Babban Fasto ya Musulunta, an koma yin Sallah a Cocinsa

Shiriya daga Allah: Babban Fasto ya Musulunta, an koma yin Sallah a Cocinsa

Wani babban Bishop a kasar Kenya ya rungumi addinin Musulunci, inda ya mayar da babban Cocinsa zuwa Masallaci, kamar yadda shafin ‘About Islam’ ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta bayyana dalilin da yasa Faston ya musulunta, inda yace ba zai jure yadda matan Kirista ke yin shigar banza ba zuwa Coci, inda ake ikirarin bautan Ubangiji.

KU KARANTA: Ba nakasashhe, sai kasashshse: Kalli abinda wasu guragu ke yi a Kaduna don cin abinci

“Sunan Coci na ‘Cocin Ubangiji na Nyalgosi’ amma yanzu ya koma ‘Masallacin Juma’a na Nyalgosi’, kamar yadda Malam Ismael Okwany wanda a baya sunansa Charles Okwany ya shaida.

Shiriya daga Allah: Babban Fasto ya Musulunta, an koma yin Sallah a Cocinsa
Ismael Okwany

A baya nayi yawo kasashe da suka hada da Malindi, Mombasa, Nairobi da Tanzania don yin da’awar addinin Kirista, don haka ina samun damar karantar dabi’un Musulmai da Kiristoci a duk inda naje, da haka na tabbatar Musulunci shine addinin gaskiya.

“Littafin Baibul ya hana Kirista sanya kayan banza, musamman wand aka iya jan ra’ayin Namiji a Coci, amma abin haushi sai gashi wasu matan Kirista na zuwa Coci da shigar banza.” Inji Malam Ismael.

Shiriya daga Allah: Babban Fasto ya Musulunta, an koma yin Sallah a Cocinsa
Okwany tare da waus mabiyansa suna Sallah a farfajiyar Cocin

Oknawy yace duk kokarin da yayi na wayar da kan Kirista akan daina sanya kayan banza yaci tura, inda yace ya fara muradin shiga Musulunci ne tun bayan daya kai ma shugaban Musulama garin Kisii ziyara, inda ya bayyana masa bukatarsa, shi kuma ya kai shi gaban Limamin Rangwe, Mustafa Saoke.

A ranar 26 ga watan Satumba ne Okwanya ya karbi Musulunci, tare da mabiyansa su 23, inda ya mayar da Cocinsa zuwa Masallacin Juma’a, kuma a yanzu haka ya Musuluntar da mutane 30 a Masallacinsa.

Daga karshe Okwany ya bayyana burinsa na ganin ya karanci Musuluci da kyau, don haka yace “Zan je in cigaba da karantar addinin Musulunci, don in samu ilimin fara da’awar addinin Musulunci.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Online view pixel