Alamu dake nuna mutum na dauke da cutar kyandar biri

Alamu dake nuna mutum na dauke da cutar kyandar biri

A yayin da masana kiwon lafiya suka dukufa wajen binciken ainihin magani wannan cuta ta kyandar biri, masana kiwon lafiya sun bankado alamomi da ke bayyana a jikin mai dauke da wannan cuta.

Akwai bayyanar kuraje da zarar kwayoyin cutar sun gama kyankyasar su a jikin dan Adam. Ita wannan cuta ta daukan kimanin makonnin uku a jikin mutum kafin ta warke.

Da yawan masu dauke da wannan cuta sun samo ta ne ta hanyar mu'amala da dabbobi dake yawo cikin dajika.

Legit.ng ta kawo muku jerin alamomi dake bayyana a jikin mai dauke da cutar kyandar biri

1. A mataki na farko, wato daga kwana 1 zuwa 5:

Zazzabi, ciwon kai mai tsanani, kumburin gabbai, ciwon baya, ciwon jiki da kuma rashin kuzari a jiki.

2. Mataki na biyu, wato daga kwana 5 zuwa 10:

Bayyanar kuraje musamman ma a fuska sannan sai su yadu a sauran sassa na jiki

3. Mataki na uku, wato kwana 10 zuwa 21:

Cikin wannan kwanaki ne kananun kuraje za su fara jan ruwa tare da kaikayi kamar maruru.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel