Kwamacala: Wani Malamin Firamari daya faɗi jarabawa a Kaduna ya sake kwatawa

Kwamacala: Wani Malamin Firamari daya faɗi jarabawa a Kaduna ya sake kwatawa

Daya daga cikin Malaman Firamari a jihar Kaduna ya bara, inda ya mayar da martani game da batun gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufai yayi na cewa su 21,780 sun fadi jarabawar gwaji.

Malamin mai suna Calipha Ibrahim Abdullahi ya bayyana damuwarsa ne a shafin Facebook, inda yace bai yar da bayanan gwamnan ba, inda yace wani salo ne gwamnati ta fito da shi don ganin ta muzanta ma Malamai.

KU KARANTA: Wata Kotun Musulunci ta yi fatali da ƙarar da aka shigar da Sheikh Kabiru Gombe a Kano

Kwamacala: Wani Malamin Firamari daya faɗi jarabawa a Kaduna ya sake kwatawa

Calipha

Sai dai NAIJ.com ta ruwaito yadda Malam Calipha ya bayyana ra’ayin nasa da yaren turanci a shafin na Facebook bai yi kama da wanda ya dace ace yana koyar da dalibai ba, ko da ma na Firamari.

Don kuwa Malam Calipha ya nuna rashin kwarewa tsagwaranta wajen iya amfani da yaren turanci, balle kuma a baka, wanda da shine yaren daya kamata yayi amfani da shi wajen koyar da daliban nasa.

Ga dai yadda Malam Calipha yayi bayanin nasa a shafinsa na Facebook, ya rage ma mai karatu yayi alkalanci, ko wannan bawan Allah ya cancanci koyar da daliban Firamari?

Kwamacala: Wani Malamin Firamari daya faɗi jarabawa a Kaduna ya sake kwatawa

Bayanin Calipha

Sai dai da dama daga cikin yan Najeriya sun nuna bacin ransu game da manufar gwamnatin jihar na sallamar Malaman da suka fadi jarabawar kamar yadda gwamnan jihar ya bayyana, wasu na gani kamata yayi a baiwa Malaman horo, wasu na ganin ya dace a sake gwada su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel