Jami'an tsaro sun samu makamai masu guba a gidan Nnamdi Kanu

Jami'an tsaro sun samu makamai masu guba a gidan Nnamdi Kanu

Jami'an 'yan sandan Najeriya sun kwarmata cewa a yayin wani samamen ba-zata da suka kai a gidan hatsabibin nan shugaban kungiyar yan aware mai fafutukar ganin an raba Najeriya ta IPOB mai sunan Nnamdi Kanu sun samu wasu makamai masu guba.

Kwamishinan yan sandan jihar ta Abia mai suna Anthony Ogbizi dai shine ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai inda ya bayyana cewa daga cikin makaman da suka gano a gidan na sa sun hada da wasu samfurin bama-bamai da kuma bindiga bazazzaga.

Jami'an tsaro sun samu makamai masu guba a gidan Nnamdi Kanu

Jami'an tsaro sun samu makamai masu guba a gidan Nnamdi Kanu

KU KARANTA: Majalisar wakilai zata binciki ministan noma

NAIJ.com ta samu dai cewa Mista Ogbizi ya kuma bayyana cewa duk dai a yayin samamen da suka kai a ranar Lahadin da ta gabata, sun kuma samu wasu tarin takardu da kuma wasiku haramtattu da suke bayyana sirrukan kungiyar da ma shire-shiren su na nan gaba.

Haka ma dai Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewa jami'an yan sanda ne da sauran hadakar sauran jami'an tsaron kasar suka yi hadin gwiwa suka yi samamen sakamakon wani bayanin sirri da suka samu daga wasu mutanen gari da suka bayyana masu cewa har yanzu yan kungiyar ta IPOB suna taruwa a gidan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel