Dandalin Kannywood: Rayuwar dakin miji ta fi ta fim dadi - Fati Ladan

Dandalin Kannywood: Rayuwar dakin miji ta fi ta fim dadi - Fati Ladan

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa a masa,antar Kannywood watau Fati Ladan ta kwarmatawa majiyar mu cewa rayuwar Auren da ta samu kanta a ciki ta fiye mata rayuwar fim din da tayi a shekarun baya dadi da muhimmanci.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi wakilin majiyar mu a kwanakin baya kimanin shekaru hudu kenan bayan tayi aure ta dena sana'ar yin fim din.

Dandalin Kannywood: Rayuwar dakin miji ta fi ta fim dadi - Fati Ladan

Dandalin Kannywood: Rayuwar dakin miji ta fi ta fim dadi - Fati Ladan

KU KARANTA: Ni na sa hannu a kwangilolin NNPC

NAIJ.com dai ta samu cewa jarumar a cikin firar ta kuma shawarci sauran jarumai mata na masana'antar fim din a wannan lokaci da su kame kan su su kuma maida hankali sosai wajen gudanar da sana'ar ta su saboda a cewar ta lokacin 'ya mace a masana'antar dan karami ne.

Haka ma dai jarumar Fati Ladan ta bayyana kuma cewa a ra'ayin ta yawan da 'yan matan fim din ne suka yi musamman ma yara masu kananan shekaru yake jawo kuruciya da yawa a masana'antar.

Fati Ladan dai ta yi aure ne kimanin shekaru hudu da suka gabata inda Allah ya azurta ta da samun da namiji amma daga baya ya rasu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel