Shugaba Buhari ya sake sababbin nadin mukamai 2 na kasar nan

Shugaba Buhari ya sake sababbin nadin mukamai 2 na kasar nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Mista Uchehi N. Orji a matsayin shugaban cibiyar kasuwanci ta Nigerian Sovereign Investment Authority, NSIA.

An nada Mista Orji a watan Oktoba na shekarar 2012 wanda ya shafe shekaru biyar yana shugabantar cibiyar a karo na farko, wanda a yanzu bisa ga tanadi da tsarin kasa karkashin sashe na 16 na cibiyar ta NSIA, akwai damar kara sake shekaru biyar a karo na biyu.

Shugaba Buhari ya sake sababbin nadi

Shugaba Buhari ya sake sababbin nadi

NAIJ.com ta fahimci cewa, a shekarun da ya shafe yana shugabantar wannan cibiya, yayi bajintu kwarai da aniyya wanda a yanzu cibiyar ta na da kima ta kusan Dalar Amurka Biliyan 2

A yayin haka dai, shugaba Buhari ya tabbatar da zabin Farfesa Hayatu Chiroma a matsayin shugaban makarantan koyon shari'a Nigerian Law School.

KARANTA KUMA: Sunaye 17 dake nuna alakar kabilancin Buhari da Jonathan wajen nade-nade a kamfanin NNPC

Fafesa Chiroma zai maye gurbin Mista Olanrewaju Onadeko sakamakon lokacin sa na ajiye aiki da yayi.

A yadda hadimin shugaban kasa akan harkokin ganawa da menema labarai da al'umma Femi Adesina, ya bayyana cewa Chiroma Farfesa ne a kan harkar shari'a, wanda a yanzu shine mataimakin shugaban makarantar koyon shari'a ta garin Yola a jihar Adamawa.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel