Sanata Shehu Sani ya caccaki Buhari da majalisar ministoci

Sanata Shehu Sani ya caccaki Buhari da majalisar ministoci

Sanatan dake wakiltar majabar jihar Kaduna ta tsakiya kuma dan jam'iyyar APC a majalisar dattijai Sanata Shehu Sani ya caccaki matakin da shugaba Buhari da kuma majalisar zartarwa ta ministoci game da hana ma'aikata albashin su muddun suna yajin aiki.

Sanatan da yake tsokaci game da hakan a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook a jiya ya bayyana matakin a matsayin abunda bai dace ba kuma ba da yawun sa ba.

Sanata Shehu Sani ya caccaki Buhari da majalisar ministoci

Sanata Shehu Sani ya caccaki Buhari da majalisar ministoci

KU KARANTA: Yan matan Chibok na Jami'a - Osinbajo

NAIJ.com ta samu dai cewa Sanata Shehu ya ci gaba da cewa: "A lokacin da muke yan adawa mun yi yaki da irin wannan kudurin sannan kuma muka goyi bayan kar a tsaida albashin ma'aikata don sun tafi yajin aiki."

Daga karshe kuma sai Sanatan ya bayyana cewa hana ma'aikata albashin su don kawai suna neman karin kyautatuwar muhallin aiki mai inganci ba zai kawo maslaha ba ko kadan sai ma kara tabarbarewa lamurra.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel