Gwamnatin tarayya ta yanke wa 'yan Boko Haram 20 mummunan hukunci

Gwamnatin tarayya ta yanke wa 'yan Boko Haram 20 mummunan hukunci

Wata kotu a Najeriya ta yanke wa akalla mutune ashirin (20) hukuncin daurin shekaru biyar zuwa shekaru takwas a gidan yari bayan da ta same su da laifin zama cikin kungiyar nan ta ta'addanci da akewa lakabi da Boko Haram.

Mun dai samu daga majiyoyin mu da dama cewa kotun da ta ke zaman ta a asirce a cikin wata babbar cibiya ta sojoji da ke a garin Kainji na jihar Neja ce ta yanke wannan hukunci.

Gwamnatin tarayya ta yanke wa 'yan Boko Haram 20 mummunan hukunci

Gwamnatin tarayya ta yanke wa 'yan Boko Haram 20 mummunan hukunci

KU KARANTA: Buhari ya karrama jakadu 3 na kasashen ketare

NAIJ.com ta samu cewa kuma kotun ta wanke wasu mutanen fiye da tamanin 80 saboda da rashin samun gamsassun kwararran hujjoji da ke tabbatar da cewa su yan Boko Haram din ne.

Sai dai kuma kamar dai yadda gwamnatin ta tarayya ta tsara tun kwanan baya, ba za a saki mutanen da kotun ta wanke ba har sai an yi masu wani shiri na musamman da zai raba su da tsattsauran ra'ayoyin su da kuma gyara halayensu tukuna.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel