Rikita-Rikita: Majalisar wakilai zata binciki ministan noma da hukumar kwastam

Rikita-Rikita: Majalisar wakilai zata binciki ministan noma da hukumar kwastam

Yan majalisar wakilan Najeriya sun sha alwashin bincikar ministan albarkatun gona da kuma hukumar hana fasa-kwouri watau kwastam ta kasa bisa fitar da rubabbar doyar da akayi zuwa kasar waje daga Najeriya.

Majalisar ta wakillai dai ta ba kwamitocin ta biyu dake kula da harkokin noman da kuma hukumar kwastam din alhakin bincikar jami'an da abun ya shafa a hukumomin da nufin lalubo yadda akayi sakaci har hakan ta faru da nufin magance matsalar.

Rikita-Rikita: Majalisar wakilai zata binciki ministan noma da hukumar kwastam

Rikita-Rikita: Majalisar wakilai zata binciki ministan noma da hukumar kwastam

KU KARANTA: Wata malamar asibita na shirin sayar da yaro N15,000

NAIJ.com dai ta samu cewa wadanda aka dorawa kwamitocin alhakin ya bincika akan lamarin sun hada da shugaban hukumar dake kula da harkokin fita da kayayyaki, shugaban hukumar dake kula da ingancin kayayyaki da ma dai dukkan wadanda lamarin ya shafa.

Wannan matakin na majalisar wakilai dai na zuwa ne bayan da dan majalisar mai wakiltar mazabar sa daga jihar Nasarawa Jonathan Gaza ya gabatar da wani kuduri kan lamarin da ya bayyana a matsayin abin kunya da kuma daga hankali.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel