An kaiwa wani Kwanturola na hukumar Fasakauri hari a jihar Ogun

An kaiwa wani Kwanturola na hukumar Fasakauri hari a jihar Ogun

Sani Madugu wanda shine kwanturola na hukumar Fasakauri ta Najeriya reshen jihar Ogun, ya tsallake rijiya da baya sakamakon wani hari da wasu 'yan ta'adda suka kai masa a ranar talatar da gabata a kan wata babbar hanya.

Mista Madugu yayin dawowa zuwa Idiroko daga birnin Abeokuta tare da ma'aikantan hukumar guda takwas ma su tsaronsa, 'yan ta'addan suka farma motocin su da misalin karfe 8:00 na dare.

An kaiwa wani Kwanturola na hukumar Fasakauri hari a jihar Ogun

An kaiwa wani Kwanturola na hukumar Fasakauri hari a jihar Ogun

Kwanturolan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis ta yau yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar ta fasakauri dake Idiroko, inda ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun ribaci cinkoson motoci akan babbar hanyar Ijako wajen kawowa mu su wannan mugun hari.

A cewar Madugu, 'yan ta'adda sun rugurguza motocinsu tare da kwatar kayan sanyawa na daya daga cikin ma'aikatansu mai sunan David Ojo.

KARANTA KUMA: Mu na tantamar yadda ake gudanar da shari'ar 'yan Boko Haram a sirrance - Kungiyar Amnesty International

Ya ke cewa, wannan harin da 'yan ta'adda ba zai sanya hukumar ta rage matsawa ma su shigo da kaya ta barauniyar hanya ba, domin ana zargin wannan harin 'yan sumogalin ne suka yi shi.

NAIJ.com ta ruwaito daga kwanturolan cewa, hukumar ta yi nasarar datse buhu 1000 na shinkafar kasar turai tare da garwar mai guda 200 da kuma wasu motoci na alfarma da aka shigo da su kasar nan ba bisa ka'ida ba.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel