Majalisar dattijai ta yi dokar da zata bata damar rantsar da shugaban kasa da mataimakin sa

Majalisar dattijai ta yi dokar da zata bata damar rantsar da shugaban kasa da mataimakin sa

Majalisar dattijai ta zartar da wata doka da zata canja al'adar nan ta rantsar da zababben shugaban kasa a filin taro na Eagle square zuwa zauren majalisar.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, ne ya bijiro da kudirin kafin daga bisani ya sami sahalewar majalisar bayan 'yan majalisar sun tafka mahawara a kan sa.

Majalisar dattijai ta yi dokar da zata bata damar rantsar da shugaban kasa da mataimakin sa

Majalisar dattijai ta yi dokar da zata bata damar rantsar da shugaban kasa da mataimakin sa

Yayin karanta sabuwar dokar, shugaban kwamitin, Abdul-Aziz Nyako, ya bayyana cewar da zarar dokar ta samu amincewar majalisar wakilai, rantsar da zababben shugaban kasa a filin taro yazo karshe. Abdul-Aziz ya kara da cewa rantsar da shugaban kasa a majalisar zai fi kai waye domin majalisar ta tattara wakilai daga kowanne bangaren kasa.

DUBA WANNAN: Batun sata a hukumar JAMB, ko dai sharota kawai Kemi Adeosun tayi?

Bayan kammala mahawara, majalisar ta amince da kudirin, saidai ta cire wani bangare na kudirin da ya nemi gabatar da wasu addu'o'i yayin rantsar da shugaban kasa da mataimakin sa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel