Kasar Amurka ta fice daga kungiyar kasashen duniya ta UNESCO bisa zargin nunawa Isra'ila wariya

Kasar Amurka ta fice daga kungiyar kasashen duniya ta UNESCO bisa zargin nunawa Isra'ila wariya

Tun a shekarar 2011 kasar Amurka ta datse fiye da rabin tallafin kudi da take bawa kungiyar ta UNESCO saboda shawarar da kungiyar ta yanke na bawa kasar Falasdin cikakkiyar damar zama 'yar kungiyar.

Ita dai kungiyar ta UNESCO tana karkashin kulawar majalisar dinkin duniya ne, kuma ita ce keda alhakin mallakawa kasashen duniya wuraren tarihi kamar irin su Palmyra dake kasar Siriya da Grand Canyon na kasar Amurka.

Shugabar kungiyar UNESCO ta bayyana cewar basu ji dadin matakin da kasar Amurka ta dauka ba, saidai ta bayyana cewar ficewar kasar ta Amurka yana da nasaba da siyasa.

Duk da kasar ta Amurka ta bayyana ficewarta daga kungiyar UNESCO, zata cigaba da zama cikin kungiyar har zuwa karshen shekarar 2018.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya taya Zanna Mustapha murnar cin lambar yabo na kungiyar UNHCR

Tun a farkon shekarar nan ne firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya soki kungiyar UNESCO bayan data bayyana yankin tsohon birnin Hebron dake gabar yammacin Falasdin a matsayin gadon duniya.

Kasar ta Isra'ila, tun a shekarar data gabata, ta bayyana yanke duk wata hulda tsakanin ta da kungiyar UNESCO bayan da kungiyar ta amince da wani kuduri da yaki alakanta jinsin yahudawa da wani bangaren bauta mai tsarki dake Jerusalem, tare da bayyana haramcin wasu al'amuran kasar Isra'ila a yankin gabar yammacin Falasdin.

Wata jarida mai nazarin tattalin kasashen duniya ta bayyana cewar kasar Amurka ta yanke shawarar ficewar ne domin ta samu damar adana kudi, domin kasar ta Amurka na samarwa da kungiyar UNESCO kudi har Dala miliyan 80 duk shekara.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel