Har yanzu muna cigaba da neman daliban nan 5 da suka nutse a ruwa, inji hukumar 'yan sanda ta jihar Kaduna

Har yanzu muna cigaba da neman daliban nan 5 da suka nutse a ruwa, inji hukumar 'yan sanda ta jihar Kaduna

- 'Yan sandar jihar Kaduna na cigaba da nemo yaran da suka nutse a ruwa

- Daliban sun kai ziyara hukumar samar da ruwa ne a jihar Kaduna

- Bin matakan tsaro na da matukar anfani don tsare lafiya, hukumar 'yan sanda ta shaida

Har yanzu hukumar 'yan sandar jihar Kaduna na cigaba da neman yara 5 da suka nutse a ruwa yayin ziyarar bude ido da suka kai a hukumar samar da ruwa.

Aliyu Mukhtar ma’aikaci a hukumar ‘yan sanda ta jihar Kadunan ya tabbatar da afkuwan lamarin, yayin da yake bayyana cewa suna jin faruwar hakan ne ‘yan sanda suka bazama neme su, sun yi kokarin ceto wasu yaran da malamai biyu a cikin su.

Har yanzu muna cigaba da neman yara 5 da suka bata- Hukumar 'yan Sanda

Har yanzu muna cigaba da neman yara 5 da suka bata- Hukumar 'yan Sanda

Ma’aikacin ya shaidawa gidan jaridar Daily Trust cewa hukumar makarantar bata sanar dasu zasu tafi yawon bude ido ba amma sai da hatsarin ya faru suka ji labari

Daga wata majiya Naij.com ta sami rahoton cewa daliban tare da malaman su sun ziyarci hukumar samar da ruwa a Malali ta jihar Kaduna da niyyar zasu hau wani kwale-kwale da bashi da kwari don su tsallaka kogin.

Saboda yawan da suka yi a cikin kwale-kwalen ne da rashin kwarinsa yasa suka nitse. A cikin su wadanda suka iya iyo ne suka ceto wasu amma har yanzu wasu ba a samo su ba.

DUBA WANNAN: Bin kwakwap: Shin ko cikin bayanan Buhari na murnar samun 'yancin kai akwai zuqi-ta malle a ciki?

Ya shaida cewa suna iya bakin kokarin su wajen ganin sun ceto yaran da suka nitse. 'A yanzu haka muna cigaba da neman sauran yaran daba a gani ba' Mukhtar ya shaida.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel