Ma'aikaciyar jinya ta hada baki da wasu ma'aurata wajen siyar da yaro

Ma'aikaciyar jinya ta hada baki da wasu ma'aurata wajen siyar da yaro

- Malamar Asibiti da hadin bakin wasu ma'aurata sun yi shirin sayan yaro dan shekaru 5 kan kudi naira 15,000

- Mahaifiyar yaron ne ta hada baki da hukumar 'yan sanda aka samu nasarar damke masu sayan

- Malamar asibitin ta ce ma'auratan sun zo Kano daga Jihar Rivers ne don samun yaron da zasu goya

A jiya ne hukumar 'yan sandan Jihar Kano ta bayyana wasu mutane 3 da su ka hada baki don sayan wani yaro dan shekaru 5. Hukumar ta samu damke su ne a ranar 10 ga watan Oktoba bisa rahoto da mahaifiyar yaron ta shigar a hukumar.

Mai magana da yawun hukumar, DSP Magaji Majiya, ya ce hukumar ta hada baki da mahaifiyar yaron mai suna Hajiya Fatima na ta amince cinikin ya gudana na sayar da yaron kan kudi naira15000, a inda aka bada naira 13000 na shigar ciniki.

Ma'aikaciyar jinya ta hada baki da wasu ma'aurata wajen siyar da yaro

Ma'aikaciyar jinya ta hada baki da wasu ma'aurata wajen siyar da yaro

An nan ne aka yi ram da daya daga cikin masu laifin mai suna Itopam Pious. Itopam ta yi ikirarin ita malamar asibitin ido ne na ECWA ta jihar Kano kuma ta amsa laifin nata.Ta ce ta sayan ma wasu ma'aurata ne 'yan Jihar Rivers.

DUBA WANNAN: Arewa ne zata fitar da Shugaban Kasa a 2019 - Orji Kalu

Ta ce ma'auratan masu suna Mista da Misis Charles Bob-manuel sun zo Kano ne don samun yaron da zasu goya sakamakon basu taba haihuwa ba na tsawon shekaru 12. Ma'autan dai sun ki amsa laifin da ake zargin su da shi.

Majiya ya ce bincike dai na cigaba da gudana kuma za'a gurfanar da su gaban kotu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel