Fadar El-Rufa'i ta malamai sun fadi jarrabawa farfaganda ce kawai - Kungiyar kwadago

Fadar El-Rufa'i ta malamai sun fadi jarrabawa farfaganda ce kawai - Kungiyar kwadago

Kungiyar kwadago reshen jihar Kaduna ta yi korafi ga gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufa'i kan yadda ya bayyanawa idon duniya cewa kashi biyu cikin uku na malaman makarantun firamaren jihar sa sun fadi jarrabawar 'yan aji hudu.

Mallam El-Rufa'i ya bayyana hakan yayin karbar wata tawagar baki daga bankin duniya da suka kawo fadar ta shi ziyara a ranar Litinin din da ta gabata.

Gwamnan ya ce, "mun jarraba malaman firamare 33, 000, mu ba su jarrabawa 'yan aji hudu wanda muke bukatar nasarar su a kaso 75 na jarrabawar, sai dai abin takaici shine kaso 66 cikin 100 daga cikinsu sun fadi wannan jarrabawa".

Ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta sallami malamai 20, 000 da basu cancanta ba, tare da diban guda 25, 000 domin tallafo harkar karatu sakamakon zagwanyewa kasa da ya ke.

Fadar El-Rufa'i ta malamai sun fadi jarrabawa farfaganda ce kawai - Kungiyar kwadago

Fadar El-Rufa'i ta malamai sun fadi jarrabawa farfaganda ce kawai - Kungiyar kwadago

Shugaban kungiyar ta kwadago Adamu Ango ya bayyana shafin Premium Times cewa, gwamnan ya yi kuskurin a wannan tonan silili da ya yi.

Baya ga zama shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Kaduna, Ango kuma shine sakatare na kungiyar malamai, inda ya ke kalubalantar gwamnan akan ya bayyana sakamakon wannan jarrabawa tare da cewa gwamnan bai yi abinda ya dace ba wajen yiwa malaman tonan silili a fili.

KARANTA KUMA: Buhari ne ya bani damar aiki da Naira Biliyan 640 yayin da yake kasar Landan - Baru

Ango ya ce, gwamnan a matsayinsa na mai bayar da aiki ba shi da hurumin zama mai tantancewa, kuma wannan jarrabawa hurumin cibiyar malamai ta kasa ce (Teachers Registration Councik, TRCN) ta gudanar da ita cikin tsarukan da suka kamata.

Shugaban kungiyar ya cigaba da cewa, a madadin wannan jarrabawa da gwamnatin ta gudanar, kamata ya yi ta kawo wani tsari na horar da malaman kan makamin aikinsu, daga nan sai ta tantance wadanda ba su mayar da hankali da daukan abin da muhammanci ba.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel