ALLAHU AKBAR: Aljani ya karbi musulunci a hannun Sheikh Dahiru Bauchi

ALLAHU AKBAR: Aljani ya karbi musulunci a hannun Sheikh Dahiru Bauchi

- Bakin Aljanin ya karbi musulunci alhali ya na jikin wani bil-adama ne

- Aljanin ya yi magana da murya kasa-kasa kowa na jin sa

- Shehin malamin ya canja ma aljanin mai suna Chinike zuwa Muhammadu Mustapha bayan musuluntar sa

Wani aljani mai suna Chineke ya karbi musulunci a hannun shahararren Shehin Darika, Dahiru Usman Bauchi. Chineke dai ya musulunta ne yayin da ya shiga jikin wani dan Jihar Bauchi mai suna Babangida.

Bayan musuluntar nasa, Dahiru Bauchi ya umurce sa da yi wanka na shigowa musulunci. Ya canza masa suna zuwa Muhammadu Mustapha. Ya kuma yi masa addu'ar tabbatuwa cikin musulunci.

ALLAHU AKBAR: Aljani ya karbi musulunci a hannun Sheikh Dahiru Bauchi

ALLAHU AKBAR: Aljani ya karbi musulunci a hannun Sheikh Dahiru Bauchi

Chineke ya yi magana kasa-kasa kowa na jin sa lokacin da yake karban musulunci. Ya kuma ce a da yana bin addinin kirista ne kaman sauran 'yan gidan su.

DUBA WANNAN: Ra'ayoyin 'yan Arewa game da yi wa kasa garanbawul sun banbanta

Bayan amsar musuluncin aljanin, manema labarai sun tambayi shehin yadda za'a tabbatar da cewa lallai aljani ne ya karbi musuluncin, sai shehin ya ce Alkur'ani da musulmai suka yi imani da shi, ya tabbatar da aljannu duk da mutane ba su iya ganin su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel