Osinbajo ya sa baki a game da rikicin Baru da Kachikwu inda ya wanke NNPC

Osinbajo ya sa baki a game da rikicin Baru da Kachikwu inda ya wanke NNPC

- Farfesa Yemi Osinbajo yayi magana game da rikicin NNPC

- A cewar Farfesa Osinbajo ya sa hannu a lokacin yana rike da kasar

- Akwai rade-radin an buga badakala a Kamfanin NNPC na kasar

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya sa baki a game da rikicin Maikanti Baru da Ibe Kachikwu inda ya wanke Kamfanin NNPC.

Osinbajo ya sa baki a game da rikicin Baru da Kachikwu

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo a ofis

Mataimakin Shugaban kasa ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da bakin sa Laolu Akande. Farfesa Osinbajo ya bayyana cewa shi ya sa hannu a kan kwangilolin NNPC a lokacin da Shugaban kasa Buhari yake jinya a Landan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yana tare da Shugaban NNPC

Akwai rade-radin an buga badakala a Kamfanin NNPC bayan da wata wasika da Ministan man kasar ya aikawa Shugaba Buhari ta fita fili. Akande a shafin sa na Tuwita yace an sa hannu kan kwangilolin ne domin biyan wasu bashi da Gwamnatin ta gada.

Mai magana da yawun Shugaba Goodluck Jonathan ya sa baki game da rikicin Shugaban NNPC Maikanti Baru da kuma Ministan mai Ibe Kachikwu a wani rubutu da yayi a wannan makon inda yace tun farko Shugaba Buhari yayi kuskure.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel