Wani mutum ya yanke wa kanwar sa kai a jihar Benuwe

Wani mutum ya yanke wa kanwar sa kai a jihar Benuwe

- Fushi yasa wani matashi ya yanke wa kanwar sa kai a Benuwe

- Matasan garin Otukpa sun kama mai laifin ne a lokacin da yake kokarin guduwa bayan yayi kisan kai

- Dattawan garin suka ceci rayuwan Jonah daga hanun fusatattun matasan da suka kama shi

Wani matashi mai suna Jonah ya yankewa kanwar sa kai a Otukpa dake karamar hukumar Ogbadibo a jihar Benuwe.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa, Jonah wanda ake zargin sa da tabun hankali, ya yanke kan kanwar sa ne ta dalilin musu da ya shiga tsakanin su a safiyar yau Alhamis.

Wani mutum ya yanke wa kanwar sa kai a jihar Benuwe

Wani mutum ya yanke wa kanwar sa kai a jihar Benuwe

Shugaban matasan garin Johnson Agada ya fada ma yan jarida cewa, matasan garin suka kama mai laifin a lokacin da yake kokarin guduwa bayan ya kashe kanwar sa.

KU KARANTA : An kashe dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afrika ta Kudu

Dattawan garin suka ceci rayuwar Jonah daga hannun fusattatun matasan da suka kama shi a lokacin da yake kokarin guduwa.

A lokacin da yan jarida suka tunkari mai magana da yawon rudunar yansadar jihar, Moses Yamu dan samun cikakken bayyani, game da al'marin, ya fada musu cewa bai da wata masaniya game da aukuwan lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel