An farfasa kwalaben giya 475 a karamar hukumar Kazauren jihar Jigawa

An farfasa kwalaben giya 475 a karamar hukumar Kazauren jihar Jigawa

- An farfasa kwalaben giya 475 a karamar hukumar Kazaure a Jigawa

- Hukumar Hisbah ta yi hani da shaye-shaye a jihar

- Wasu matasan sun maida sayar da kayen maye sana'a

Karamar hukumar Kazaure dake jihar Jigawa ta farfasa kwalaben giya 475 da jarkokin ire-iren giya a garin.

Alhaji Magaji Muhammad na ofishin yada labarai na hukumar ya shaida hakan a ranar Alhamis a garin Dutse. Rundunar ‘yan Hisbah ne suka cafke kwalaben daga hannun masu saidawa a wasu unguwoyin.

An farfasa kwalaben giya 475 a karamar hukumar Kazaure a Jigawa

An farfasa kwalaben giya 475 a karamar hukumar Kazaure a Jigawa

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta hana siyar da giya da miyagun kwayoyi da kuma shan giya a cikin gari.

Alhaji Muammad ya shaida cewa an fasa kwalaben giya 377, jarkokin burkutu 37 da kuma wasu kwalaben kayan maye 101.

A cewar Alhaji Jamilu Uwais, ciyaman na majalisar karamar hukumar ne 'duk masu saida giya da kayan maye su daina ko kuwa su fuskanci mummunar tuhuma daga shari’a.’

Alhaji Uwais ya shaida cewa majalisar zata cigaba da yaki da hani da saida kayan maye da shan su a fadin jihar.

DUBA WANNAN: Shehu Sani na da jaa, kan batun ciwo uban bashi da Buhari zayyi

A karshe kuwa Alhaji Muhammad ya shaida cewa shugaban taron yana kara bawa samari da matasa shawara kan daina shaye-shayen miyagun kwayoyi da kayan maye domin kuwa yana lahani ga jikin dana Adam.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel