Wasu Ma'aikata Jihar Ekiti sun koka da Gwamna Fayose

Wasu Ma'aikata Jihar Ekiti sun koka da Gwamna Fayose

- Ma'aikatan a Jihar Ekiti sun koka da Gwamnan Jihar ma-ci

- Jami'an sun ce sun gwammace tsohon Gwamna Kayode Fayemi

- Ma'aikatan sun bayyana yadda Fayemi ya kara masu albashi

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Ma'aikatan Jihar Ekiti su na kuka da Gwamnan Jihar Ayodele Peter Fayose.

Wasu Ma'aikata Jihar Ekiti sun koka da Gwamna Fayose

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Fayemi

Wata Kungiya ta Ma'aikatan Jihar Ekiti karkashin lemar EWF ta koka da yadda su ke fama da Gwamnan Ekiti. Ma'aikatan sun ce ba su samun wani romo a karkashin Gwamnatin Gwamna Ayodele Peter Fayose.

KU KARANTA: An tsige Kwamishinonin Jihar Neja

Shugaban Kungiyar Mike Bamidele ya bayyana wannan a wata hira da yayi a gidan rediyo inda ya bayyana cewa a lokacin Gwamna Kayode Fayemi an karawa Ma'aikatan lafiya da wasun su a Jihar albashi har sau 4.

A cewar sa dai Shugabannin Kungiyoyin ma'aikatan su gaza nemowa jama'a 'yancin su a fadin Jihar. A mulkin Fayemi dai har tsofaffin ma'aikata an karawa albashi amma a karkashin Gwamnatin mai ci kuwa sai dai labari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel