Gwamnatin Jihar Neja ta tsige kusan duka Kwamishinonin ta

Gwamnatin Jihar Neja ta tsige kusan duka Kwamishinonin ta

- Gwamnan Jihar Neja ya sauke kaf Kwamishinonin sa a jiya

- Gwamna Abubakar Bello zai nada wasu Kwamishinonin nan gaba

- Kwamishinoni 3 ne rak su ka sha a zazzagar da Gwamnan yayi

Mun samu labari cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello yayi zazzaga a Gwamnatin sa.

Gwamnatin Jihar Neja ta tsige kusan duka Kwamishinonin ta

Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello yayi zazzagar gaske inda ya sauke kaf Kwamishinonin Jihar ban da guda 3 rak. Wadanda su ka sha su ne kurum wadanda aka nada kwanan nan.

KU KARANTA: Sanatoci sun ba Gasar World Cup muhimmanci

Guda 3 da ba a tsige ba su ne Kwamishinan al'adu da shakatawa da kuma Kwamishinan ma'adanai da kuma na harkar ruwa. Gwamnan ya bayyana wannan ne a taron da yayi da Majalisar zartarwa na Jihar.

Gwannan ya nemi Kwamishinonin su mikawa Sakatororin din-din-din kayan aiki kafin a nada wasu. Gwamna Abubakar Bello ya dai dage taron da aka saba na mako-mako har sai an nada sababbin Kwamishinoni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel