Tsohon gwamnan jihar Taraba ya gaskata kashe kudi Naira biliyan 1.6 ba a cikin kasafin kudin gwamnati ba

Tsohon gwamnan jihar Taraba ya gaskata kashe kudi Naira biliyan 1.6 ba a cikin kasafin kudin gwamnati ba

- Tsohon gwamnan jihar Taraba ya gaskata kashe kudi Naira biliyan 1.6 da ba a cikin kasafin kudin gwamnati ba

- Hukumar yaki da cin hanci na tuhumar tsohon gwamnan da barnatar da kudin gwamnati

- Tsohon gwamnan ya musa zargin da ake masa na badakalar kashe Naira biliyan 1.6

Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame ya fito ya shaida cewa kashe kudin da baya cikin kasafin kudi ba laifi bane yayin gudanar da ayyukkan gwamnati domin kuwa dole akwai karin kasafin kudi a cikin kudin gwamnati.

Kotun Gudu da ke birnin tarayya ce ta tsayar da shi akan zargin sa da ake da wadaka da Naira biliyan 1.6 yayin dake gwamnan jihar. Mista Nyame ya shaida cewa ya bi hanyar gaskiya ne wajen kashe kudin gwamnatin lokacin mulkin sa.

Tsohon gwamnan Taraba ya gaskata kashe kudi Naira biliyan 1.6 da ba a cikin kasafin kudi ba

Tsohon gwamnan Taraba ya gaskata kashe kudi Naira biliyan 1.6 da ba a cikin kasafin kudi ba

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ce ta kama tsohon gwamnan da zargin barnatar da kudin jihar Taraba yayin da yake gwmnan jihar. Hukumar na tuhumarsa da kashe kudin da baya cikin kasafin kudi a matsayin aikata aikin dai-dai. Ya kashe kudi lokacin mulkinsa har Naira milyan 982.

A cewar Nyame kuwa ‘kasafin kudi a kimance suke ne kawai, da kara jaddadawa yayi aiki lokacinsa duk da ya zarce a kashe kudi ba a cikin kasafin kudin gwamnaitin ba.’

Akwai kudade da dama da aka bawa ofishin gwamnan amma gwamnatin ta kashe fiye da abin da ta samu daga majalisar dokoki da wasu manyan ma’aikatu.

Kotun ta tuhume Nyame da ko ya san cewa babban laifi ne aikata hakan, gwamnan ya ansa da cewa ya sani amma sai dai idan babu wani kari a cikin kasafin kudin.

DUBA WANNAN: Masu ababen hawa a Kano sun koka da jami'an hukumar KAROTA da 'yan sanda

Nyame ya ce zarcewa a kashe kudi daga cikin kasafin kudi ba komai bane lokacin aikata ayyukan gwamnati domin kuwa dole akwai karin kasafin kudi.

Mai shari’ar Adebukola Banjoko ya dage karar zuwa 12 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel