Ma su ikrarin cewa za a maida Najeriya kasar muslunci suna yin haka dan neman mukami – Kadinal Onaiyekan

Ma su ikrarin cewa za a maida Najeriya kasar muslunci suna yin haka dan neman mukami – Kadinal Onaiyekan

- Onaiyekan ya soki masu ikrarin cewa za a mayar da Najeriya kasar Musulunci

- Kadinal Onaiyikan ya ce Babu wanda zai samu nasara idan rikici ya barke tsakanin musulmai da kristoci

- Shugaban cocin Katolika ya shawarci kristoci su zama masu hakuri da abokan zaman su

Shugaban darikar cocin Katolika na birnin tarayya Abuja, Kadinal John Onaiyekan ya soki wadanda suke ikrarin cewa za a mayar da Najeriya kasar muslunci, da neman mukami.

Kadinal Onaiyekan ya bayyana haka ne a taron fahimta juna tsakanin cocin darikar Angilica da cocin Katolika da ya halarta a ranar 11 ga watan Oktoba.

Kuma ya gargadi kristoci da cewa, idan rikici ya barke tsakanin musulmai da kristoci a Najeriya babu wanda zai yi nasara.

Ma su ikrarin cewa za a maida Najeriya kasar muslunci suna yin haka dan neman mukami – Kadinal Onaiyekan

Ma su ikrarin cewa za a maida Najeriya kasar muslunci suna yin haka dan neman mukami – Kadinal Onaiyekan

Ya kara da cewa: “Kristocin kasar nan suna addinin su a cikin sauki, kuma babu mai takura mu su, kuma suna zuwa wurare dabandaban yin da’awa.

KU KARANTA : Wata matar aure ta tona asirin Faston cocin su da ye neme ta a shafin Whatsapp

“Saboda haka ina mamakin ma su cewa gwamnatin na kokarin mayar da Najeriya kasar muslunci, ta yaya haka zai iya faruwa?

“Duk lokacin da aka ba musulmi mukami a Najeriya, sai mu ce ana musuluntar da kasar, saboda haka mu ma ,mu shirya jin martanin musulmai duk lokacin da aka ba krista mukami.

“Irin wadanan mutanen ke bata ma addinin krista suna.

"Saboda haka ina ba kristocin Najeriya shawara da su kasance masu hakuri da abokan zaman su, musamman mabiya addinin muslunci,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel