Badakalar Naira Biliyan 640: Kamfanin NNPC na zargin Osinbajo da sanya hannu

Badakalar Naira Biliyan 640: Kamfanin NNPC na zargin Osinbajo da sanya hannu

Har yanzu shiru ake ji kamar mutuwa ta gifta a ofishin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sakamakon badakalar kudin kamfanin Man fetur na NNPC da aka rasa dalilin salwantar su, wanda wannan kudi sun tashi Biliyan 640 a kudin Najeriya.

Badakalar Naira Biliyan 640: Kamfanin NNPC na zargin Osinbajo da sanya hannu

Badakalar Naira Biliyan 640: Kamfanin NNPC na zargin Osinbajo da sanya hannu

Tun a makonnin da suka gabata, an yi ta korafi kan yadda shugaban NNPC Maikanti Baru ya yi amfani da wannan makudan kudi ba tare da yardar magabantansa ba, wanda wasu rahotannin suka bayyana cewa shugaba Buhari ne ya bayar da wannan izini a yayin da da yake kasar Landan wajen duba lafiyarsa.

Wannan tuhuma ta janyo maganganu da dama daga wajen masu ruwa da tsaki da kuma masu dillancin labarai.

KARANTA KUMA: Mu na tantamar yadda ake gudanar da shari'ar 'yan Boko Haram a sirrance - Kungiyar Amnesty International

Shafin Premium Times ya ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne kakakin kamfanin NNPC Ndu Ughamadu ya busa algaitarsa kan cewa mataimakin shugaban kasa ne ya bayar da izinin aiwatar da aiki da wannan makudan kudi a kamfanin.

Sai dai har yanzu ofishin mataimakin shugaban kasar ya yi shiru domin bayyana "i ko a'a" dangane da wannan fasa kwan da kamfanin na NNPC ya yi.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel