Hukumar IMF ta gargadi Najeriya kan hauhawan bashin da a ke bin ta

Hukumar IMF ta gargadi Najeriya kan hauhawan bashin da a ke bin ta

- Hukumar Asusun Bayar da Lamuni ta Duniya (IMF), ta gargadi Najeriya da wasu kasashen bisa hauhawan bashin da a ke bin su

- Hukmar ta ce sai Najeriya ta yi da gaske zata iya fita cikin wannan kangi na bashi

- A irin wannan hali ne Shugaba Buhari ya bukaci 'yan Majalisar su bada damar ciwon bashi na dalan Amurka biliyan 5.5

A jiya ne Hukumar Asusun Bayar da Lamuni ta Duniya ta gargadi Gwamnatin Najeriya kan hauhawan bashin da ake bin ta, musamman wanda ta ranto daga kasashen waje.

Ta ce bashin zai zama matsala ga Najeriya da kasashen irin ta masu karamin karfi idan har ba su kula da yadda za su habaka tattalin arzkin su ba.

Hukumar IMF ta gargadi Najeriya kan hauhawan bashin da a ke bin ta

Hukumar IMF ta gargadi Najeriya kan hauhawan bashin da a ke bin ta

Ya zuwa watan Yuni na wannan shekara, bashin da ake bin Najeriya ya kai na naira tiriliyon 19.63. A irin wannan hali ne kuma Shugaba Buhari ya bukaci Majalisar Tarayya ta amince da ciwo bashin biliyan 5.5 na dalan Amurka.

DUBA WANNAN: Ra'ayoyin 'yan Arewa game da yi wa kasa garanbawul sun banbanta

Hukumar ta ce akwai hanyoyi da Najeriya zata bi don bunkasa tattalin arzikin ta. Ta shawarci Najeriya da ta habaka tattalin arzikin ta koma bayan man fetur.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel