Ma'aikatan bada agaji sun fice daga Gwoza bayan harin da Boko Haram ta kai

Ma'aikatan bada agaji sun fice daga Gwoza bayan harin da Boko Haram ta kai

- Ma'aikatan agaji da yawa sun tatara kayan su sun fice daga garin Gwoza da ke jihar Borno

- Sun fice daga garin ne bayan kungiyar Boko Haram sunyi yinkurin fada wa garin a daren Talata

- Yan ta'addan sun tsere bayan musayan harsashi da sukayi da hafsoshin rundunar sojin Najeriya na lokaci mai tsawo

Ma'aikatan bada agaji sun tsere daga garin Gwoza da ke jihar Borno bayan kungiyar Boko Haram ta kai hari mai tsanani a garin a daren Litinin.

A tsakanin shekarar 2014 - 2015, garin Gwoza ne babban birnin daular islama da kungiyar Boko Haram ta kafa, amma bayan Rundunar sojin Najeriya ta kwace garin daga hannun yan ta'addan, dimbin masu aikin agaji sun iso garin domin taimakawa mutanen da sukayi gudun hijira da kuma wadanda fitinar da shafa.

Ma'aikatan bada agaji sun tsere da Borno bayan harin da Boko Haram ta kai

Ma'aikatan bada agaji sun tsere da Borno bayan harin da Boko Haram ta kai

A wata hira da wani mazaunin garin Gwoza mai suna John Ali yayi da jaridar Thisday a jiya Laraba, ya shaida musu cewa yan ta'addan suyi kokarin fada wa garin amma hafsoshin rundunar sojin Najeriya suka kora su. Wannan artabun da akayi ne yasa dimbin ma'aikatan bada agajin suka tatara kayayakin su suka fice daga garin.

KU KARANTA: Buhari yaci amanar musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

Ya kara da cewa ficewa ma'aikatan agajin zai haifar da matsalar karancin abinci, magunguna da ma wasu kayayakin more rayuwa wadda dama su ke taimakawa mutanen garin dashi musamman wanda suka dawo daga gudun hijira.

Yace mafi yawancin mazauna garin baza su gudu ba duk da sun razana da harin domin rundunar sojin Najeriya ta tabbatar musu cewa zasuyi duk mai yiwuwa domin kare rayukan su da dukiyoyin su.

Yan ta'addan sunyi niyyar fada ma garin ne ta yankin Yamteke, inda dama a shekarun baya ta wannan hanyan ne suka kawo hari a garin. Yan ta'addar da yawa sun sami raunuku bayan musayan wuta da sukayi da sojojin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel