Yawon shakatawa: Wasu 'yan makarantar sakandare 5 sun nutse a cikin kogin Kaduna

Yawon shakatawa: Wasu 'yan makarantar sakandare 5 sun nutse a cikin kogin Kaduna

- Dalibar 5 suka nutsar a kogin Kaduna a ranar Laraba yayin da suke yawon shakatawa

- 'Yan makarantar sun hada da maza 4 da mace daya

- Lamarin ta faru a lokacin da injimin jirgin ruwa wanda yake jawo ruwa ta baci

Akalla dalibai 5 daga makarantar sakandare masu zaman kansu a Kaduna suka nutsar a cikin kogin Kaduna yayin da suke yawon shakatawa a safiyar ranar Larabar, 11 ga watan Oktoba.

'Yan makarantar, maza 4 da mace daya suka nutsar a daidai karfe 11 na safe a lokacin da suka tafi yawon shakatawa a yankin, wata majiyar gwamnatin ta shaida wa NAIJ.com.

Kogin Kaduna ita ce iyaka wanda ta raba al’ummar Hausa-Fulani a arewa da ‘yan kabilar kudancin Kaduna.

Yawon shakatawa: Wasu 'yan makarantar sakandare 5 sun nutse a cikin kogin Kaduna

Kogin Kaduna inda wasu dalibai suka nutse

Bisa ga majiyar, wannan lamarin ya faru ne lokacin da injimin jirgin ruwa wanda yake jawo ruwa daga kogi zuwa jirgin ya samu damuwa yayin da dalibai suke tafiya a cikin ruwa.

KU KARANTA: El-Rufai ya bayyana yadda za’a cimma sake fasalin al’amuran kasa

Yawancin dalibai sun jikkata, yayin da ba a san inda mutane biyar suke ba har zuwa lokacin wannan rahoton.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel