El-Rufai ya bayyana yadda za’a cimma sake fasalin al’amuran kasa

El-Rufai ya bayyana yadda za’a cimma sake fasalin al’amuran kasa

- Mallam Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya yi magana akan fafutukar dake kudu maso gabashin Najeriya

- El-Rufai yace wadanda ke wakiltan masu fafutukan sun kasance yan tsiraru a yankin don haka akoda yaushe masu rinjaye ke nasara

- Ya kara fa cewa babban rashin adalci shine kokarin sanya daidai ya zamo ba daidai ba da kuma sanya wand aba daidai bay a zamo daidai

A ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba, Mallam Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna yace zai zamo babban rashin adalcin yin fafutuka domin “sanya daidai ya zamo wanda ba daidai” saboda wakilan masu fafutuka sun kasance yan tsiraru.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a Abuja yayinda yake yi wa wadanda suka halarci wani taro da kwamitin jamhuriya na gaskiya na jam’iyyar APC ta shirya maraba da zuwa.

KU KARANTA KUMA: Al’umman Gwoza sunyi biki don nasarar sojoji akan yan Boko Haram (hotuna/bidiyo)

Ya kuma kara da cewa a duk wani al’amari masu rinjaye kanyi nasara akan yan tsiraru.

A halin yanzu, NAIJ.com ta rahoto cewa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bayyana cewa arewa bata jin tsoron sake fasalin al’amuran Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel